نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4018 | 38 | 48 | واذكر إسماعيل واليسع وذا الكفل وكل من الأخيار |
| | | Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu. |
|
4019 | 38 | 49 | هذا ذكر وإن للمتقين لحسن مآب |
| | | Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma. |
|
4020 | 38 | 50 | جنات عدن مفتحة لهم الأبواب |
| | | Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su. |
|
4021 | 38 | 51 | متكئين فيها يدعون فيها بفاكهة كثيرة وشراب |
| | | Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã. |
|
4022 | 38 | 52 | وعندهم قاصرات الطرف أتراب |
| | | Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna. |
|
4023 | 38 | 53 | هذا ما توعدون ليوم الحساب |
| | | Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi. |
|
4024 | 38 | 54 | إن هذا لرزقنا ما له من نفاد |
| | | Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwarMu ce, bã ta ƙãrẽwa. |
|
4025 | 38 | 55 | هذا وإن للطاغين لشر مآب |
| | | Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma. |
|
4026 | 38 | 56 | جهنم يصلونها فبئس المهاد |
| | | Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita. |
|
4027 | 38 | 57 | هذا فليذوقوه حميم وغساق |
| | | Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini. |
|