نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4014 | 38 | 44 | وخذ بيدك ضغثا فاضرب به ولا تحنث إنا وجدناه صابرا نعم العبد إنه أواب |
| | | Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne. |
|
4015 | 38 | 45 | واذكر عبادنا إبراهيم وإسحاق ويعقوب أولي الأيدي والأبصار |
| | | Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurninMu) da basĩra. |
|
4016 | 38 | 46 | إنا أخلصناهم بخالصة ذكرى الدار |
| | | Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira). |
|
4017 | 38 | 47 | وإنهم عندنا لمن المصطفين الأخيار |
| | | Kuma lalle sũ a wurinMu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta. |
|
4018 | 38 | 48 | واذكر إسماعيل واليسع وذا الكفل وكل من الأخيار |
| | | Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu. |
|
4019 | 38 | 49 | هذا ذكر وإن للمتقين لحسن مآب |
| | | Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma. |
|
4020 | 38 | 50 | جنات عدن مفتحة لهم الأبواب |
| | | Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su. |
|
4021 | 38 | 51 | متكئين فيها يدعون فيها بفاكهة كثيرة وشراب |
| | | Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã. |
|
4022 | 38 | 52 | وعندهم قاصرات الطرف أتراب |
| | | Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna. |
|
4023 | 38 | 53 | هذا ما توعدون ليوم الحساب |
| | | Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi. |
|