نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4005 | 38 | 35 | قال رب اغفر لي وهب لي ملكا لا ينبغي لأحد من بعدي إنك أنت الوهاب |
| | | Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. |
|
4006 | 38 | 36 | فسخرنا له الريح تجري بأمره رخاء حيث أصاب |
| | | Sabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa. |
|
4007 | 38 | 37 | والشياطين كل بناء وغواص |
| | | Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.) |
|
4008 | 38 | 38 | وآخرين مقرنين في الأصفاد |
| | | Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa. |
|
4009 | 38 | 39 | هذا عطاؤنا فامنن أو أمسك بغير حساب |
| | | Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike. |
|
4010 | 38 | 40 | وإن له عندنا لزلفى وحسن مآب |
| | | Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma. |
|
4011 | 38 | 41 | واذكر عبدنا أيوب إذ نادى ربه أني مسني الشيطان بنصب وعذاب |
| | | Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba." |
|
4012 | 38 | 42 | اركض برجلك هذا مغتسل بارد وشراب |
| | | Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã. |
|
4013 | 38 | 43 | ووهبنا له أهله ومثلهم معهم رحمة منا وذكرى لأولي الألباب |
| | | Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali. |
|
4014 | 38 | 44 | وخذ بيدك ضغثا فاضرب به ولا تحنث إنا وجدناه صابرا نعم العبد إنه أواب |
| | | Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne. |
|