نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3985 | 38 | 15 | وما ينظر هؤلاء إلا صيحة واحدة ما لها من فواق |
| | | Kuma waɗannan bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani. |
|
3986 | 38 | 16 | وقالوا ربنا عجل لنا قطنا قبل يوم الحساب |
| | | Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike." |
|
3987 | 38 | 17 | اصبر على ما يقولون واذكر عبدنا داوود ذا الأيد إنه أواب |
| | | Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwanMu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne. |
|
3988 | 38 | 18 | إنا سخرنا الجبال معه يسبحن بالعشي والإشراق |
| | | Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã. |
|
3989 | 38 | 19 | والطير محشورة كل له أواب |
| | | Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi. |
|
3990 | 38 | 20 | وشددنا ملكه وآتيناه الحكمة وفصل الخطاب |
| | | Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima da rarrabẽwar magana. |
|
3991 | 38 | 21 | وهل أتاك نبأ الخصم إذ تسوروا المحراب |
| | | Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci? |
|
3992 | 38 | 22 | إذ دخلوا على داوود ففزع منهم قالوا لا تخف خصمان بغى بعضنا على بعض فاحكم بيننا بالحق ولا تشطط واهدنا إلى سواء الصراط |
| | | A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya." |
|
3993 | 38 | 23 | إن هذا أخي له تسع وتسعون نعجة ولي نعجة واحدة فقال أكفلنيها وعزني في الخطاب |
| | | "Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana." |
|
3994 | 38 | 24 | قال لقد ظلمك بسؤال نعجتك إلى نعاجه وإن كثيرا من الخلطاء ليبغي بعضهم على بعض إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وقليل ما هم وظن داوود أنما فتناه فاستغفر ربه وخر راكعا وأناب |
| | | (Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah. |
|