نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3954 | 37 | 166 | وإنا لنحن المسبحون |
| | | "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." |
|
3955 | 37 | 167 | وإن كانوا ليقولون |
| | | Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, |
|
3956 | 37 | 168 | لو أن عندنا ذكرا من الأولين |
| | | "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." |
|
3957 | 37 | 169 | لكنا عباد الله المخلصين |
| | | "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." |
|
3958 | 37 | 170 | فكفروا به فسوف يعلمون |
| | | Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. |
|
3959 | 37 | 171 | ولقد سبقت كلمتنا لعبادنا المرسلين |
| | | Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. |
|
3960 | 37 | 172 | إنهم لهم المنصورون |
| | | Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. |
|
3961 | 37 | 173 | وإن جندنا لهم الغالبون |
| | | Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. |
|
3962 | 37 | 174 | فتول عنهم حتى حين |
| | | Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. |
|
3963 | 37 | 175 | وأبصرهم فسوف يبصرون |
| | | Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. |
|