نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3924 | 37 | 136 | ثم دمرنا الآخرين |
| | | Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. |
|
3925 | 37 | 137 | وإنكم لتمرون عليهم مصبحين |
| | | Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. |
|
3926 | 37 | 138 | وبالليل أفلا تعقلون |
| | | Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? |
|
3927 | 37 | 139 | وإن يونس لمن المرسلين |
| | | Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
|
3928 | 37 | 140 | إذ أبق إلى الفلك المشحون |
| | | A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. |
|
3929 | 37 | 141 | فساهم فكان من المدحضين |
| | | Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. |
|
3930 | 37 | 142 | فالتقمه الحوت وهو مليم |
| | | Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
|
3931 | 37 | 143 | فلولا أنه كان من المسبحين |
| | | To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, |
|
3932 | 37 | 144 | للبث في بطنه إلى يوم يبعثون |
| | | Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. |
|
3933 | 37 | 145 | فنبذناه بالعراء وهو سقيم |
| | | Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. |
|