نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3906 | 37 | 118 | وهديناهما الصراط المستقيم |
| | | Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. |
|
3907 | 37 | 119 | وتركنا عليهما في الآخرين |
| | | Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. |
|
3908 | 37 | 120 | سلام على موسى وهارون |
| | | Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. |
|
3909 | 37 | 121 | إنا كذلك نجزي المحسنين |
| | | Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
|
3910 | 37 | 122 | إنهما من عبادنا المؤمنين |
| | | Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. |
|
3911 | 37 | 123 | وإن إلياس لمن المرسلين |
| | | Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
|
3912 | 37 | 124 | إذ قال لقومه ألا تتقون |
| | | A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" |
|
3913 | 37 | 125 | أتدعون بعلا وتذرون أحسن الخالقين |
| | | "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" |
|
3914 | 37 | 126 | الله ربكم ورب آبائكم الأولين |
| | | "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" |
|
3915 | 37 | 127 | فكذبوه فإنهم لمحضرون |
| | | Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). |
|