نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3893 | 37 | 105 | قد صدقت الرؤيا إنا كذلك نجزي المحسنين |
| | | "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
|
3894 | 37 | 106 | إن هذا لهو البلاء المبين |
| | | Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. |
|
3895 | 37 | 107 | وفديناه بذبح عظيم |
| | | Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. |
|
3896 | 37 | 108 | وتركنا عليه في الآخرين |
| | | Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. |
|
3897 | 37 | 109 | سلام على إبراهيم |
| | | Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. |
|
3898 | 37 | 110 | كذلك نجزي المحسنين |
| | | Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
|
3899 | 37 | 111 | إنه من عبادنا المؤمنين |
| | | Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
|
3900 | 37 | 112 | وبشرناه بإسحاق نبيا من الصالحين |
| | | Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. |
|
3901 | 37 | 113 | وباركنا عليه وعلى إسحاق ومن ذريتهما محسن وظالم لنفسه مبين |
| | | Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). |
|
3902 | 37 | 114 | ولقد مننا على موسى وهارون |
| | | Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. |
|