نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
389 | 3 | 96 | إن أول بيت وضع للناس للذي ببكة مباركا وهدى للعالمين |
| | | Kuma lalle ne, ¦aki na farko da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga tãlikai. |
|
390 | 3 | 97 | فيه آيات بينات مقام إبراهيم ومن دخله كان آمنا ولله على الناس حج البيت من استطاع إليه سبيلا ومن كفر فإن الله غني عن العالمين |
| | | A cikinsa akwai ãyõyi bayyanannu; (ga misãli) matsayin Ibrãhĩma. Kuma wanda ya shige shi yã kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦ãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai. |
|
391 | 3 | 98 | قل يا أهل الكتاب لم تكفرون بآيات الله والله شهيد على ما تعملون |
| | | Ka ce: "Ya kũ Mutãnen Littãfi! Don me kuke kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa Allah Mai shaida ne a kan abin da kuke aikatãwa?" |
|
392 | 3 | 99 | قل يا أهل الكتاب لم تصدون عن سبيل الله من آمن تبغونها عوجا وأنتم شهداء وما الله بغافل عما تعملون |
| | | Ka ce: "Ya ku Mutãnen Littãfi! Don me kuke taushe wanda ya yi ĩmani, daga hanyar Allah, kuma kunã nẽman ta zama karkatacciya, alhãli kuwa kunã mãsu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatãwa ba yana Masani." |
|
393 | 3 | 100 | يا أيها الذين آمنوا إن تطيعوا فريقا من الذين أوتوا الكتاب يردوكم بعد إيمانكم كافرين |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗã'aga wani ɓangare daga waɗanda aka bai wa Littãfi, zã su mayar da ku kãfirai a bãyan ĩmãninku! |
|
394 | 3 | 101 | وكيف تكفرون وأنتم تتلى عليكم آيات الله وفيكم رسوله ومن يعتصم بالله فقد هدي إلى صراط مستقيم |
| | | Kuma yãyã kuke kãfircẽwa alhãli kuwa anã karanta ãyõyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nẽmi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya. |
|
395 | 3 | 102 | يا أيها الذين آمنوا اتقوا الله حق تقاته ولا تموتن إلا وأنتم مسلمون |
| | | Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, a kan hakkin binsa da taƙawa, kuma kada ku mutu fãce kuna mãsu sallamawa (Musulmi). |
|
396 | 3 | 103 | واعتصموا بحبل الله جميعا ولا تفرقوا واذكروا نعمت الله عليكم إذ كنتم أعداء فألف بين قلوبكم فأصبحتم بنعمته إخوانا وكنتم على شفا حفرة من النار فأنقذكم منها كذلك يبين الله لكم آياته لعلكم تهتدون |
| | | Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu. |
|
397 | 3 | 104 | ولتكن منكم أمة يدعون إلى الخير ويأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر وأولئك هم المفلحون |
| | | Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alhẽri, kuma suna umurnida alhẽri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, sũ ne mãsu cin nasara. |
|
398 | 3 | 105 | ولا تكونوا كالذين تفرقوا واختلفوا من بعد ما جاءهم البينات وأولئك لهم عذاب عظيم |
| | | Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma. |
|