نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3877 | 37 | 89 | فقال إني سقيم |
| | | Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." |
|
3878 | 37 | 90 | فتولوا عنه مدبرين |
| | | Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. |
|
3879 | 37 | 91 | فراغ إلى آلهتهم فقال ألا تأكلون |
| | | Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? |
|
3880 | 37 | 92 | ما لكم لا تنطقون |
| | | "Me ya sãme ku, bã ku magana?" |
|
3881 | 37 | 93 | فراغ عليهم ضربا باليمين |
| | | Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. |
|
3882 | 37 | 94 | فأقبلوا إليه يزفون |
| | | Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. |
|
3883 | 37 | 95 | قال أتعبدون ما تنحتون |
| | | Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, |
|
3884 | 37 | 96 | والله خلقكم وما تعملون |
| | | "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" |
|
3885 | 37 | 97 | قالوا ابنوا له بنيانا فألقوه في الجحيم |
| | | Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." |
|
3886 | 37 | 98 | فأرادوا به كيدا فجعلناهم الأسفلين |
| | | Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. |
|