نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3874 | 37 | 86 | أئفكا آلهة دون الله تريدون |
| | | "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" |
|
3875 | 37 | 87 | فما ظنكم برب العالمين |
| | | "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" |
|
3876 | 37 | 88 | فنظر نظرة في النجوم |
| | | Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. |
|
3877 | 37 | 89 | فقال إني سقيم |
| | | Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." |
|
3878 | 37 | 90 | فتولوا عنه مدبرين |
| | | Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. |
|
3879 | 37 | 91 | فراغ إلى آلهتهم فقال ألا تأكلون |
| | | Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? |
|
3880 | 37 | 92 | ما لكم لا تنطقون |
| | | "Me ya sãme ku, bã ku magana?" |
|
3881 | 37 | 93 | فراغ عليهم ضربا باليمين |
| | | Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. |
|
3882 | 37 | 94 | فأقبلوا إليه يزفون |
| | | Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. |
|
3883 | 37 | 95 | قال أتعبدون ما تنحتون |
| | | Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, |
|