نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3869 | 37 | 81 | إنه من عبادنا المؤمنين |
| | | Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. |
|
3870 | 37 | 82 | ثم أغرقنا الآخرين |
| | | Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. |
|
3871 | 37 | 83 | وإن من شيعته لإبراهيم |
| | | Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. |
|
3872 | 37 | 84 | إذ جاء ربه بقلب سليم |
| | | A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. |
|
3873 | 37 | 85 | إذ قال لأبيه وقومه ماذا تعبدون |
| | | A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" |
|
3874 | 37 | 86 | أئفكا آلهة دون الله تريدون |
| | | "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" |
|
3875 | 37 | 87 | فما ظنكم برب العالمين |
| | | "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" |
|
3876 | 37 | 88 | فنظر نظرة في النجوم |
| | | Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. |
|
3877 | 37 | 89 | فقال إني سقيم |
| | | Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." |
|
3878 | 37 | 90 | فتولوا عنه مدبرين |
| | | Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. |
|