نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3864 | 37 | 76 | ونجيناه وأهله من الكرب العظيم |
| | | Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. |
|
3865 | 37 | 77 | وجعلنا ذريته هم الباقين |
| | | Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. |
|
3866 | 37 | 78 | وتركنا عليه في الآخرين |
| | | Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. |
|
3867 | 37 | 79 | سلام على نوح في العالمين |
| | | Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. |
|
3868 | 37 | 80 | إنا كذلك نجزي المحسنين |
| | | Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
|
3869 | 37 | 81 | إنه من عبادنا المؤمنين |
| | | Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. |
|
3870 | 37 | 82 | ثم أغرقنا الآخرين |
| | | Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. |
|
3871 | 37 | 83 | وإن من شيعته لإبراهيم |
| | | Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. |
|
3872 | 37 | 84 | إذ جاء ربه بقلب سليم |
| | | A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. |
|
3873 | 37 | 85 | إذ قال لأبيه وقومه ماذا تعبدون |
| | | A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" |
|