نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3850 | 37 | 62 | أذلك خير نزلا أم شجرة الزقوم |
| | | Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? |
|
3851 | 37 | 63 | إنا جعلناها فتنة للظالمين |
| | | Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. |
|
3852 | 37 | 64 | إنها شجرة تخرج في أصل الجحيم |
| | | Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. |
|
3853 | 37 | 65 | طلعها كأنه رءوس الشياطين |
| | | Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. |
|
3854 | 37 | 66 | فإنهم لآكلون منها فمالئون منها البطون |
| | | To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. |
|
3855 | 37 | 67 | ثم إن لهم عليها لشوبا من حميم |
| | | Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. |
|
3856 | 37 | 68 | ثم إن مرجعهم لإلى الجحيم |
| | | Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. |
|
3857 | 37 | 69 | إنهم ألفوا آباءهم ضالين |
| | | Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. |
|
3858 | 37 | 70 | فهم على آثارهم يهرعون |
| | | Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. |
|
3859 | 37 | 71 | ولقد ضل قبلهم أكثر الأولين |
| | | Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. |
|