نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3836 | 37 | 48 | وعندهم قاصرات الطرف عين |
| | | Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. |
|
3837 | 37 | 49 | كأنهن بيض مكنون |
| | | Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. |
|
3838 | 37 | 50 | فأقبل بعضهم على بعض يتساءلون |
| | | Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. |
|
3839 | 37 | 51 | قال قائل منهم إني كان لي قرين |
| | | Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." |
|
3840 | 37 | 52 | يقول أإنك لمن المصدقين |
| | | Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" |
|
3841 | 37 | 53 | أإذا متنا وكنا ترابا وعظاما أإنا لمدينون |
| | | "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" |
|
3842 | 37 | 54 | قال هل أنتم مطلعون |
| | | (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" |
|
3843 | 37 | 55 | فاطلع فرآه في سواء الجحيم |
| | | Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. |
|
3844 | 37 | 56 | قال تالله إن كدت لتردين |
| | | Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." |
|
3845 | 37 | 57 | ولولا نعمة ربي لكنت من المحضرين |
| | | "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." |
|