نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3826 | 37 | 38 | إنكم لذائقو العذاب الأليم |
| | | Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. |
|
3827 | 37 | 39 | وما تجزون إلا ما كنتم تعملون |
| | | Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
|
3828 | 37 | 40 | إلا عباد الله المخلصين |
| | | Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
|
3829 | 37 | 41 | أولئك لهم رزق معلوم |
| | | Waɗannan sunã da abinci sananne. |
|
3830 | 37 | 42 | فواكه وهم مكرمون |
| | | 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. |
|
3831 | 37 | 43 | في جنات النعيم |
| | | A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. |
|
3832 | 37 | 44 | على سرر متقابلين |
| | | A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. |
|
3833 | 37 | 45 | يطاف عليهم بكأس من معين |
| | | Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. |
|
3834 | 37 | 46 | بيضاء لذة للشاربين |
| | | Farã mai dãɗi ga mashãyan. |
|
3835 | 37 | 47 | لا فيها غول ولا هم عنها ينزفون |
| | | A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, |
|