نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3804 | 37 | 16 | أإذا متنا وكنا ترابا وعظاما أإنا لمبعوثون |
| | | "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? |
|
3805 | 37 | 17 | أوآباؤنا الأولون |
| | | "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" |
|
3806 | 37 | 18 | قل نعم وأنتم داخرون |
| | | Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." |
|
3807 | 37 | 19 | فإنما هي زجرة واحدة فإذا هم ينظرون |
| | | Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. |
|
3808 | 37 | 20 | وقالوا يا ويلنا هذا يوم الدين |
| | | Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." |
|
3809 | 37 | 21 | هذا يوم الفصل الذي كنتم به تكذبون |
| | | Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. |
|
3810 | 37 | 22 | احشروا الذين ظلموا وأزواجهم وما كانوا يعبدون |
| | | Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. |
|
3811 | 37 | 23 | من دون الله فاهدوهم إلى صراط الجحيم |
| | | Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. |
|
3812 | 37 | 24 | وقفوهم إنهم مسئولون |
| | | Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. |
|
3813 | 37 | 25 | ما لكم لا تناصرون |
| | | Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? |
|