نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3789 | 37 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والصافات صفا |
| | | Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). |
|
3790 | 37 | 2 | فالزاجرات زجرا |
| | | Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. |
|
3791 | 37 | 3 | فالتاليات ذكرا |
| | | Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. |
|
3792 | 37 | 4 | إن إلهكم لواحد |
| | | Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. |
|
3793 | 37 | 5 | رب السماوات والأرض وما بينهما ورب المشارق |
| | | Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. |
|
3794 | 37 | 6 | إنا زينا السماء الدنيا بزينة الكواكب |
| | | Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. |
|
3795 | 37 | 7 | وحفظا من كل شيطان مارد |
| | | Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. |
|
3796 | 37 | 8 | لا يسمعون إلى الملإ الأعلى ويقذفون من كل جانب |
| | | Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. |
|
3797 | 37 | 9 | دحورا ولهم عذاب واصب |
| | | Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. |
|
3798 | 37 | 10 | إلا من خطف الخطفة فأتبعه شهاب ثاقب |
| | | Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. |
|