نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3763 | 36 | 58 | سلام قولا من رب رحيم |
| | | "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai. |
|
3764 | 36 | 59 | وامتازوا اليوم أيها المجرمون |
| | | "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!" |
|
3765 | 36 | 60 | ألم أعهد إليكم يا بني آدم أن لا تعبدوا الشيطان إنه لكم عدو مبين |
| | | "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?" |
|
3766 | 36 | 61 | وأن اعبدوني هذا صراط مستقيم |
| | | "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya." |
|
3767 | 36 | 62 | ولقد أضل منكم جبلا كثيرا أفلم تكونوا تعقلون |
| | | "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?" |
|
3768 | 36 | 63 | هذه جهنم التي كنتم توعدون |
| | | "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita." |
|
3769 | 36 | 64 | اصلوها اليوم بما كنتم تكفرون |
| | | "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." |
|
3770 | 36 | 65 | اليوم نختم على أفواههم وتكلمنا أيديهم وتشهد أرجلهم بما كانوا يكسبون |
| | | A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
3771 | 36 | 66 | ولو نشاء لطمسنا على أعينهم فاستبقوا الصراط فأنى يبصرون |
| | | Dã Mun so, dã Mun shãfe gani daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani? |
|
3772 | 36 | 67 | ولو نشاء لمسخناهم على مكانتهم فما استطاعوا مضيا ولا يرجعون |
| | | Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba. |
|