نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3760 | 36 | 55 | إن أصحاب الجنة اليوم في شغل فاكهون |
| | | Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi. |
|
3761 | 36 | 56 | هم وأزواجهم في ظلال على الأرائك متكئون |
| | | Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira. |
|
3762 | 36 | 57 | لهم فيها فاكهة ولهم ما يدعون |
| | | Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo. |
|
3763 | 36 | 58 | سلام قولا من رب رحيم |
| | | "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai. |
|
3764 | 36 | 59 | وامتازوا اليوم أيها المجرمون |
| | | "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!" |
|
3765 | 36 | 60 | ألم أعهد إليكم يا بني آدم أن لا تعبدوا الشيطان إنه لكم عدو مبين |
| | | "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?" |
|
3766 | 36 | 61 | وأن اعبدوني هذا صراط مستقيم |
| | | "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya." |
|
3767 | 36 | 62 | ولقد أضل منكم جبلا كثيرا أفلم تكونوا تعقلون |
| | | "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?" |
|
3768 | 36 | 63 | هذه جهنم التي كنتم توعدون |
| | | "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita." |
|
3769 | 36 | 64 | اصلوها اليوم بما كنتم تكفرون |
| | | "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci." |
|