نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3754 | 36 | 49 | ما ينظرون إلا صيحة واحدة تأخذهم وهم يخصمون |
| | | Bã su jiran (kõme) fãce wata tsãwa guda, zã ta kãma su, alhãli kuwa sunã yin husũma. |
|
3755 | 36 | 50 | فلا يستطيعون توصية ولا إلى أهلهم يرجعون |
| | | Bã zã su iya yin wasiyya ba, kuma bã zã su iya kõmãwa zuwa ga iyãlansu ba. |
|
3756 | 36 | 51 | ونفخ في الصور فإذا هم من الأجداث إلى ربهم ينسلون |
| | | Kuma aka yi bũsa a cikin ƙaho, to, sai gã su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, sunã ta gudu. |
|
3757 | 36 | 52 | قالوا يا ويلنا من بعثنا من مرقدنا هذا ما وعد الرحمن وصدق المرسلون |
| | | Suka ce: "Yã bonenmu! Wãne ne ya tãyar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya." |
|
3758 | 36 | 53 | إن كانت إلا صيحة واحدة فإذا هم جميع لدينا محضرون |
| | | Ba ta kasance ba fãce wata tsãwa ce guda, sai gã su duka, sunã abin halartarwa a gare Mu. |
|
3759 | 36 | 54 | فاليوم لا تظلم نفس شيئا ولا تجزون إلا ما كنتم تعملون |
| | | To, a yau, bã zã a zãlunci wani rai da kõme ba. Kuma bã zã a sãkã muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
|
3760 | 36 | 55 | إن أصحاب الجنة اليوم في شغل فاكهون |
| | | Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi. |
|
3761 | 36 | 56 | هم وأزواجهم في ظلال على الأرائك متكئون |
| | | Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira. |
|
3762 | 36 | 57 | لهم فيها فاكهة ولهم ما يدعون |
| | | Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo. |
|
3763 | 36 | 58 | سلام قولا من رب رحيم |
| | | "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai. |
|