نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3734 | 36 | 29 | إن كانت إلا صيحة واحدة فإذا هم خامدون |
| | | Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai gã su sõmammu. |
|
3735 | 36 | 30 | يا حسرة على العباد ما يأتيهم من رسول إلا كانوا به يستهزئون |
| | | Yã nadãma a kan bãyĩNa! Wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu yi masa izgili. |
|
3736 | 36 | 31 | ألم يروا كم أهلكنا قبلهم من القرون أنهم إليهم لا يرجعون |
| | | Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutãnen) ƙarnõni a gabãninsu kuma cẽwa su bã zã su kõmo ba? |
|
3737 | 36 | 32 | وإن كل لما جميع لدينا محضرون |
| | | Kuma lalle bãbu kõwa fãce waɗanda ake halartarwa ne a wurinMu. |
|
3738 | 36 | 33 | وآية لهم الأرض الميتة أحييناها وأخرجنا منها حبا فمنه يأكلون |
| | | Kuma ãyã ce a gare su: ¡asã matacciya, Mu rãyar da ita, Mu fitar da ƙwãya daga gare ta, sai gã shi daga gare ta suke ci. |
|
3739 | 36 | 34 | وجعلنا فيها جنات من نخيل وأعناب وفجرنا فيها من العيون |
| | | Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasã), waɗansu gõnaki na dabĩno da inabõbi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga marẽmari a cikinta. |
|
3740 | 36 | 35 | ليأكلوا من ثمره وما عملته أيديهم أفلا يشكرون |
| | | Dõmin su ci 'ya'yan itãcensa, alhãli kuwa hannãyensu ba su aikata shi ba. Shin, to, bã zã su gõdẽ ba? |
|
3741 | 36 | 36 | سبحان الذي خلق الأزواج كلها مما تنبت الأرض ومن أنفسهم ومما لا يعلمون |
| | | Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasã ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba. |
|
3742 | 36 | 37 | وآية لهم الليل نسلخ منه النهار فإذا هم مظلمون |
| | | Kuma ãyã ce a gare su: Dare Muna feɗe rãna daga gare shi, sai gã su sunã mãsu shiga duhu. |
|
3743 | 36 | 38 | والشمس تجري لمستقر لها ذلك تقدير العزيز العليم |
| | | Kuma rãnã tanã gudãna zuwa ga wani matabbaci nãta. Wannan ƙaddarãwar Mabuwãyi ne, Masani. |
|