نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3723 | 36 | 18 | قالوا إنا تطيرنا بكم لئن لم تنتهوا لنرجمنكم وليمسنكم منا عذاب أليم |
| | | Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku." |
|
3724 | 36 | 19 | قالوا طائركم معكم أئن ذكرتم بل أنتم قوم مسرفون |
| | | Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi." |
|
3725 | 36 | 20 | وجاء من أقصى المدينة رجل يسعى قال يا قوم اتبعوا المرسلين |
| | | Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan. |
|
3726 | 36 | 21 | اتبعوا من لا يسألكم أجرا وهم مهتدون |
| | | "Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne." |
|
3727 | 36 | 22 | وما لي لا أعبد الذي فطرني وإليه ترجعون |
| | | "Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?" |
|
3728 | 36 | 23 | أأتخذ من دونه آلهة إن يردن الرحمن بضر لا تغن عني شفاعتهم شيئا ولا ينقذون |
| | | "Shin, zan riƙi waninSa abũbuwan bautãwa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cũta, to cẽtonsu bã ya amfanĩna da kõme, kuma bã za su iya tsãmar da ni bã." |
|
3729 | 36 | 24 | إني إذا لفي ضلال مبين |
| | | "Lalle nĩ, a lõkacin nan, tabbas, inã a cikin ɓata bayyananna." |
|
3730 | 36 | 25 | إني آمنت بربكم فاسمعون |
| | | "Lalle ni, nã yi ĩmãni da Ubangijinku, sabõda haka ku saurãre ni." |
|
3731 | 36 | 26 | قيل ادخل الجنة قال يا ليت قومي يعلمون |
| | | Aka ce (masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Dã dai a ce mutãnẽna sunã iya sani." |
|
3732 | 36 | 27 | بما غفر لي ربي وجعلني من المكرمين |
| | | "Game da gãfarar da Ubangijjĩna ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama." |
|