نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3718 | 36 | 13 | واضرب لهم مثلا أصحاب القرية إذ جاءها المرسلون |
| | | Kuma ka buga musu misãli: Waɗansu ma'abũta alƙarya, a lõkacin da Manzanni suka jẽ mata. |
|
3719 | 36 | 14 | إذ أرسلنا إليهم اثنين فكذبوهما فعززنا بثالث فقالوا إنا إليكم مرسلون |
| | | A lõkacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mũ, Manzanni ne zuwa gare ku." |
|
3720 | 36 | 15 | قالوا ما أنتم إلا بشر مثلنا وما أنزل الرحمن من شيء إن أنتم إلا تكذبون |
| | | Suka ce: "Kũ ba ku zamo bafãce mutãne ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kõme ba, ba ku zamo ba fãce ƙarya kuke yi." |
|
3721 | 36 | 16 | قالوا ربنا يعلم إنا إليكم لمرسلون |
| | | Suka ce: "Ubangijinmu Yã sani, lalle mũ, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku." |
|
3722 | 36 | 17 | وما علينا إلا البلاغ المبين |
| | | "Kuma bãbu abin da ke kanmu, fãce iyar da manzanci bayyananne." |
|
3723 | 36 | 18 | قالوا إنا تطيرنا بكم لئن لم تنتهوا لنرجمنكم وليمسنكم منا عذاب أليم |
| | | Suka ce: "Lalle mũ munã shu'umci da ku! Haƙĩƙa idan ba ku, hanu ba, haƙĩƙa, zã mu jẽfe ku, kuma haƙĩƙa wata azãba mai raɗaɗi daga gare mu zã ta shãfe ku." |
|
3724 | 36 | 19 | قالوا طائركم معكم أئن ذكرتم بل أنتم قوم مسرفون |
| | | Suka ce: "Shu'umcinku, yanã tãre da ku. Ashe, dõmin an tunãtar da ku? Ã'a, kũ dai mutãne ne mãsu ƙẽtare haddi." |
|
3725 | 36 | 20 | وجاء من أقصى المدينة رجل يسعى قال يا قوم اتبعوا المرسلين |
| | | Kuma wani mutum daga mafi nĩsan birnin ya je, yanã tafiya da gaggãwa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ku bi Manzannin nan. |
|
3726 | 36 | 21 | اتبعوا من لا يسألكم أجرا وهم مهتدون |
| | | "Ku bi waɗanda bã su tambayar ku wata ijãra kuma sũ shiryayyu ne." |
|
3727 | 36 | 22 | وما لي لا أعبد الذي فطرني وإليه ترجعون |
| | | "Kuma mene ne a gare ni, bã zan bauta wa Wanda Ya ƙãga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku?" |
|