نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3689 | 35 | 29 | إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سرا وعلانية يرجون تجارة لن تبور |
| | | Lalle waɗanda ke karãtun Littãfin Allah kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, sunã fãtan (sãmun) wani fatauci ne wanda bã ya yin tasgaro. |
|
3690 | 35 | 30 | ليوفيهم أجورهم ويزيدهم من فضله إنه غفور شكور |
| | | Dõmin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙarã musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gãfara ne, Mai gõdiya. |
|
3691 | 35 | 31 | والذي أوحينا إليك من الكتاب هو الحق مصدقا لما بين يديه إن الله بعباده لخبير بصير |
| | | Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littãfi, |
|
3692 | 35 | 32 | ثم أورثنا الكتاب الذين اصطفينا من عبادنا فمنهم ظالم لنفسه ومنهم مقتصد ومنهم سابق بالخيرات بإذن الله ذلك هو الفضل الكبير |
| | | Sa'an nan Mun gãdar da Littãfin, ga waɗanda Muka zãɓa daga bãyinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zãlunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitãwa, kuma daga cikinsu akwai mai tsẽrẽwa da ayyukan alhẽri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma. |
|
3693 | 35 | 33 | جنات عدن يدخلونها يحلون فيها من أساور من ذهب ولؤلؤا ولباسهم فيها حرير |
| | | Gidãjen Aljannar zamã sunã shigar su. Anã ƙawãce su a cikinsu, da ƙawã ta mundãye daga zĩnãriya da lu'ulu'u, kuma tufãfinsu, a cikinsu alharĩni ne. |
|
3694 | 35 | 34 | وقالوا الحمد لله الذي أذهب عنا الحزن إن ربنا لغفور شكور |
| | | Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙĩƙa Mai gafarane, Mai godiya." |
|
3695 | 35 | 35 | الذي أحلنا دار المقامة من فضله لا يمسنا فيها نصب ولا يمسنا فيها لغوب |
| | | "Wanda Ya saukar da mu a gidan zamã, daga falalarSa, wata wahala bã ta shãfar mu a cikinsa, kuma wata kãsãwa bã ta shãfar mu a cikinsa." |
|
3696 | 35 | 36 | والذين كفروا لهم نار جهنم لا يقضى عليهم فيموتوا ولا يخفف عنهم من عذابها كذلك نجزي كل كفور |
| | | Kuma waɗanda suka kãfirta sunã da wutar Jahannama, bã a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma bã a sauƙaƙa musu daga azãbarta. Kamar haka Muke sãka wa kõwane mai yawan kãfirci. |
|
3697 | 35 | 37 | وهم يصطرخون فيها ربنا أخرجنا نعمل صالحا غير الذي كنا نعمل أولم نعمركم ما يتذكر فيه من تذكر وجاءكم النذير فذوقوا فما للظالمين من نصير |
| | | Kuma sũ, sunã hargõwar nẽman ãgaji a cikinta. (Sunã cẽwa) "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance munã aikatãwa." Ashe, kuma, ba Mu rãyar da ku ba, abin da mai tunãni zai iya yin tunãni a ciki, kuma mai gargaɗi yã jẽ muku? To, ku ɗanɗana, sabõda haka bãbu wani mataimaki, ga azzãlumai. |
|
3698 | 35 | 38 | إن الله عالم غيب السماوات والأرض إنه عليم بذات الصدور |
| | | Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasã. Lalle Shĩ ne Masani ga abin da yake ainihin zukata. |
|