نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
363 | 3 | 70 | يا أهل الكتاب لم تكفرون بآيات الله وأنتم تشهدون |
| | | Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuka kãfirta da ãyõyin Allah, alhãli kuwa kũ, kuna shaida (cẽwa sũ gaskiya ne)? |
|
364 | 3 | 71 | يا أهل الكتاب لم تلبسون الحق بالباطل وتكتمون الحق وأنتم تعلمون |
| | | Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane? |
|
365 | 3 | 72 | وقالت طائفة من أهل الكتاب آمنوا بالذي أنزل على الذين آمنوا وجه النهار واكفروا آخره لعلهم يرجعون |
| | | Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ." |
|
366 | 3 | 73 | ولا تؤمنوا إلا لمن تبع دينكم قل إن الهدى هدى الله أن يؤتى أحد مثل ما أوتيتم أو يحاجوكم عند ربكم قل إن الفضل بيد الله يؤتيه من يشاء والله واسع عليم |
| | | "Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cẽwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani." |
|
367 | 3 | 74 | يختص برحمته من يشاء والله ذو الفضل العظيم |
| | | Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma'abucin falala ne, Mai girma. |
|
368 | 3 | 75 | ومن أهل الكتاب من إن تأمنه بقنطار يؤده إليك ومنهم من إن تأمنه بدينار لا يؤده إليك إلا ما دمت عليه قائما ذلك بأنهم قالوا ليس علينا في الأميين سبيل ويقولون على الله الكذب وهم يعلمون |
| | | Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri, zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane. |
|
369 | 3 | 76 | بلى من أوفى بعهده واتقى فإن الله يحب المتقين |
| | | Na'am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu taƙawa. |
|
370 | 3 | 77 | إن الذين يشترون بعهد الله وأيمانهم ثمنا قليلا أولئك لا خلاق لهم في الآخرة ولا يكلمهم الله ولا ينظر إليهم يوم القيامة ولا يزكيهم ولهم عذاب أليم |
| | | Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar ¡iyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. |
|
371 | 3 | 78 | وإن منهم لفريقا يلوون ألسنتهم بالكتاب لتحسبوه من الكتاب وما هو من الكتاب ويقولون هو من عند الله وما هو من عند الله ويقولون على الله الكذب وهم يعلمون |
| | | Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane. |
|
372 | 3 | 79 | ما كان لبشر أن يؤتيه الله الكتاب والحكم والنبوة ثم يقول للناس كونوا عبادا لي من دون الله ولكن كونوا ربانيين بما كنتم تعلمون الكتاب وبما كنتم تدرسون |
| | | Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa." |
|