نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3529 | 32 | 26 | أولم يهد لهم كم أهلكنا من قبلهم من القرون يمشون في مساكنهم إن في ذلك لآيات أفلا يسمعون |
| | | Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne? |
|
3530 | 32 | 27 | أولم يروا أنا نسوق الماء إلى الأرض الجرز فنخرج به زرعا تأكل منه أنعامهم وأنفسهم أفلا يبصرون |
| | | Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba? |
|
3531 | 32 | 28 | ويقولون متى هذا الفتح إن كنتم صادقين |
| | | Kuma sunã cẽwa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya?" |
|
3532 | 32 | 29 | قل يوم الفتح لا ينفع الذين كفروا إيمانهم ولا هم ينظرون |
| | | Ka ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba." |
|
3533 | 32 | 30 | فأعرض عنهم وانتظر إنهم منتظرون |
| | | Sabõda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, sũ ma mãsu jira ne. |
|
3534 | 33 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم يا أيها النبي اتق الله ولا تطع الكافرين والمنافقين إن الله كان عليما حكيما |
| | | Yã kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗã'ã ga kãfirai da munãfukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima. |
|
3535 | 33 | 2 | واتبع ما يوحى إليك من ربك إن الله كان بما تعملون خبيرا |
| | | Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa. |
|
3536 | 33 | 3 | وتوكل على الله وكفى بالله وكيلا |
| | | Ka dõgara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakĩli. |
|
3537 | 33 | 4 | ما جعل الله لرجل من قلبين في جوفه وما جعل أزواجكم اللائي تظاهرون منهن أمهاتكم وما جعل أدعياءكم أبناءكم ذلكم قولكم بأفواهكم والله يقول الحق وهو يهدي السبيل |
| | | Allah bai sanya zũciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya mãtanku waɗanda kuke yin zihãri daga gare su, su zama uwãyenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankãkarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu nãku, maganarku ce da bãkunanku alhãli kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shĩ ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai. |
|
3538 | 33 | 5 | ادعوهم لآبائهم هو أقسط عند الله فإن لم تعلموا آباءهم فإخوانكم في الدين ومواليكم وليس عليكم جناح فيما أخطأتم به ولكن ما تعمدت قلوبكم وكان الله غفورا رحيما |
| | | Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan'uwanku ga addini da dĩmajojinku. Kuma bãbu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukãtanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai. |
|