نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3523 | 32 | 20 | وأما الذين فسقوا فمأواهم النار كلما أرادوا أن يخرجوا منها أعيدوا فيها وقيل لهم ذوقوا عذاب النار الذي كنتم به تكذبون |
| | | Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." |
|
3524 | 32 | 21 | ولنذيقنهم من العذاب الأدنى دون العذاب الأكبر لعلهم يرجعون |
| | | Kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, mafi ƙasƙanci, kãfin a kai ga azãba mafi girma, dõmin fãtan za su kõmo. |
|
3525 | 32 | 22 | ومن أظلم ممن ذكر بآيات ربه ثم أعرض عنها إنا من المجرمين منتقمون |
| | | Kuma wãne ne ya fi zãlunci bisa ga wanda aka tunãtar da ãyõyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mũ, Mãsu yin azãbar rãmuwa ne ga mãsu laifi. |
|
3526 | 32 | 23 | ولقد آتينا موسى الكتاب فلا تكن في مرية من لقائه وجعلناه هدى لبني إسرائيل |
| | | Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã Littafi, sabõda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Banĩ Isrã'ĩla. |
|
3527 | 32 | 24 | وجعلنا منهم أئمة يهدون بأمرنا لما صبروا وكانوا بآياتنا يوقنون |
| | | Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, sunã shiryarwa da umurninMu, a lõkacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance sunã yin yaƙĩni da ãyõyinMu. |
|
3528 | 32 | 25 | إن ربك هو يفصل بينهم يوم القيامة فيما كانوا فيه يختلفون |
| | | Lalle Ubangijinka shĩ ne zai rarrabe a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa. |
|
3529 | 32 | 26 | أولم يهد لهم كم أهلكنا من قبلهم من القرون يمشون في مساكنهم إن في ذلك لآيات أفلا يسمعون |
| | | Shin, ba ya shiryar da su cẽwa da yawa Muka halakara gabãninsu, daga al'ummõmi sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi. Shin, ba su jĩ ne? |
|
3530 | 32 | 27 | أولم يروا أنا نسوق الماء إلى الأرض الجرز فنخرج به زرعا تأكل منه أنعامهم وأنفسهم أفلا يبصرون |
| | | Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle Mũ, Munã kõra ruwa zuwa ga ƙasã ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shũka wadda dabbõbinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba? |
|
3531 | 32 | 28 | ويقولون متى هذا الفتح إن كنتم صادقين |
| | | Kuma sunã cẽwa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance mãsu gaskiya?" |
|
3532 | 32 | 29 | قل يوم الفتح لا ينفع الذين كفروا إيمانهم ولا هم ينظرون |
| | | Ka ce: "Ranar hukuncin nan, ĩmãnin waɗanda suka kãfirta bã zai amfãne su ba (a cikinta) kuma bã zã a yi musu jinkiri ba." |
|