نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3514 | 32 | 11 | قل يتوفاكم ملك الموت الذي وكل بكم ثم إلى ربكم ترجعون |
| | | Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shĩ ne ke karɓar rãyukanku. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku." |
|
3515 | 32 | 12 | ولو ترى إذ المجرمون ناكسو رءوسهم عند ربهم ربنا أبصرنا وسمعنا فارجعنا نعمل صالحا إنا موقنون |
| | | Kuma da kã gani a lõkacin da mãsu laifi suke mãsu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mũ mãsu yaƙĩni ne." |
|
3516 | 32 | 13 | ولو شئنا لآتينا كل نفس هداها ولكن حق القول مني لأملأن جهنم من الجنة والناس أجمعين |
| | | Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya. |
|
3517 | 32 | 14 | فذوقوا بما نسيتم لقاء يومكم هذا إنا نسيناكم وذوقوا عذاب الخلد بما كنتم تعملون |
| | | To, ku ɗanɗana sabõda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mũ mã Mun manta da ku, kuma ku dãnɗani azãbar dawwama sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
|
3518 | 32 | 15 | إنما يؤمن بآياتنا الذين إذا ذكروا بها خروا سجدا وسبحوا بحمد ربهم وهم لا يستكبرون |
| | | Waɗanda ke ĩmãni da ãyõyinMu kawai, sũ ne waɗanda idan aka karanta musu ãyõyinMu sai su fãɗi sunã mãsu sujada kuma su yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, alhãli kuwa su bã su yin girman kai. |
|
3519 | 32 | 16 | تتجافى جنوبهم عن المضاجع يدعون ربهم خوفا وطمعا ومما رزقناهم ينفقون |
| | | Sãsanninsu nã nĩsanta daga wurãren kwanciya, sunã kiran Ubangijinsu bisa ga tsõro da ɗammãni, kuma sunã ciryawa daga abin da Muka azurta su. |
|
3520 | 32 | 17 | فلا تعلم نفس ما أخفي لهم من قرة أعين جزاء بما كانوا يعملون |
| | | Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
3521 | 32 | 18 | أفمن كان مؤمنا كمن كان فاسقا لا يستوون |
| | | Shin, wanda ya zama mũmini yanã kamar wanda ya zama fãsiƙi? Bã zã su yi daidai ba. |
|
3522 | 32 | 19 | أما الذين آمنوا وعملوا الصالحات فلهم جنات المأوى نزلا بما كانوا يعملون |
| | | Amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, sunã da gidãjen Aljannar makõma, a kan liyãfa sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
|
3523 | 32 | 20 | وأما الذين فسقوا فمأواهم النار كلما أرادوا أن يخرجوا منها أعيدوا فيها وقيل لهم ذوقوا عذاب النار الذي كنتم به تكذبون |
| | | Kuma waɗanda suka yi fãsiƙanci to makõmarsu ita ce wuta, kõ da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azãbai wutã, wadda kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." |
|