نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3474 | 31 | 5 | أولئك على هدى من ربهم وأولئك هم المفلحون |
| | | Waɗannan sunã a kan shiriya ta daga Ubangijinsu kuma waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. |
|
3475 | 31 | 6 | ومن الناس من يشتري لهو الحديث ليضل عن سبيل الله بغير علم ويتخذها هزوا أولئك لهم عذاب مهين |
| | | Kuma akwai daga cikin mutãne wanda ke sayen tãtsuniyõyi dõmin ya ɓatar da mutãne daga hanyar Allah, bã da wani ilmi ba, kuma ya riƙe ta abin izgili! Waɗancan sunã da wata azãba mai wulãkantãwa. |
|
3476 | 31 | 7 | وإذا تتلى عليه آياتنا ولى مستكبرا كأن لم يسمعها كأن في أذنيه وقرا فبشره بعذاب أليم |
| | | Kuma idan an karanta ãyõyinMu a gare shi, sai ya jũya bãya, yanã mai girman kai, kamar dai bai saurãre su ba kamar dai akwai wanĩ danni a kan kunnuwansa! To, ka yi masa bushãra da azãba mai raɗaɗi. |
|
3477 | 31 | 8 | إن الذين آمنوا وعملوا الصالحات لهم جنات النعيم |
| | | Lalle, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljannar ni'ima. |
|
3478 | 31 | 9 | خالدين فيها وعد الله حقا وهو العزيز الحكيم |
| | | Sunã dawwama a cikinsu Allah Yã yi alkawarin, Ya tabbatar da shi. Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
3479 | 31 | 10 | خلق السماوات بغير عمد ترونها وألقى في الأرض رواسي أن تميد بكم وبث فيها من كل دابة وأنزلنا من السماء ماء فأنبتنا فيها من كل زوج كريم |
| | | (Allah) Ya halitta sammai, bã da ginshiƙi wanda kuke gani ba, kuma Yã jẽfa duwatsu mãsu kafuwa a cikin ƙasã, dõmin kada ta karkata da ku kuma Ya wãtsa daga kowanc irin dabba a cikinta, kuma Mun saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka tsirar a cikinta, daga kõwane nau'i biyu (nami; i da mace) mai ban sha'awa. |
|
3480 | 31 | 11 | هذا خلق الله فأروني ماذا خلق الذين من دونه بل الظالمون في ضلال مبين |
| | | Wannan shĩ ne halittar Allah. To ku nũna mini, "Mẽne ne waɗanan da ba Shi ba suka halitta? Ã'a, azzalumai sunã a cikin ɓata bayyananna." |
|
3481 | 31 | 12 | ولقد آتينا لقمان الحكمة أن اشكر لله ومن يشكر فإنما يشكر لنفسه ومن كفر فإن الله غني حميد |
| | | Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. (Muka ce masa) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde. |
|
3482 | 31 | 13 | وإذ قال لقمان لابنه وهو يعظه يا بني لا تشرك بالله إن الشرك لظلم عظيم |
| | | Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, "Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma." |
|
3483 | 31 | 14 | ووصينا الإنسان بوالديه حملته أمه وهنا على وهن وفصاله في عامين أن اشكر لي ولوالديك إلي المصير |
| | | Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu (Muka ce masa) "Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take." |
|