نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3354 | 29 | 14 | ولقد أرسلنا نوحا إلى قومه فلبث فيهم ألف سنة إلا خمسين عاما فأخذهم الطوفان وهم ظالمون |
| | | Kuma lalle Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya zauna a cikinsu shẽkara dubu fãce shẽkara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ũfãna) ta kãmã su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. |
|
3355 | 29 | 15 | فأنجيناه وأصحاب السفينة وجعلناها آية للعالمين |
| | | Sa'an nan Muka tsĩrar da shi da mutãnen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata ãyã ga tãlikai. |
|
3356 | 29 | 16 | وإبراهيم إذ قال لقومه اعبدوا الله واتقوه ذلكم خير لكم إن كنتم تعلمون |
| | | Da Ibrãhĩm a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ku bautã wa Allah ku bĩ Shi da taƙawa. Wannan Shĩ ne alhẽri a gare ku idan kun kasance kunã sani. |
|
3357 | 29 | 17 | إنما تعبدون من دون الله أوثانا وتخلقون إفكا إن الذين تعبدون من دون الله لا يملكون لكم رزقا فابتغوا عند الله الرزق واعبدوه واشكروا له إليه ترجعون |
| | | "Abin da dai kuke bautãwa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, bã su mallakã muku arziki. Sabõda haka ku nẽmi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi gõdiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku. |
|
3358 | 29 | 18 | وإن تكذبوا فقد كذب أمم من قبلكم وما على الرسول إلا البلاغ المبين |
| | | "Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummõmi a gabãninku sun ƙaryata, kuma bãbu abin da ke kan Manzo, fãce iyar da manzanci, iyarwa bayyananna." |
|
3359 | 29 | 19 | أولم يروا كيف يبدئ الله الخلق ثم يعيده إن ذلك على الله يسير |
| | | Shin, ba su ga yadda Allah ke fãra yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah. |
|
3360 | 29 | 20 | قل سيروا في الأرض فانظروا كيف بدأ الخلق ثم الله ينشئ النشأة الآخرة إن الله على كل شيء قدير |
| | | Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda (Allah) Ya fãra yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yanã ƙãga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kõme. |
|
3361 | 29 | 21 | يعذب من يشاء ويرحم من يشاء وإليه تقلبون |
| | | "Yanã azabta wanda Ya so, kuma Yanã jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake jũyaku." |
|
3362 | 29 | 22 | وما أنتم بمعجزين في الأرض ولا في السماء وما لكم من دون الله من ولي ولا نصير |
| | | "Kuma ba ku zamo mãsu buwãya ba a cikin ƙasã, kuma haka a cikin sama kuma bã ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki." |
|
3363 | 29 | 23 | والذين كفروا بآيات الله ولقائه أولئك يئسوا من رحمتي وأولئك لهم عذاب أليم |
| | | Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan sunã da wata azãba mai raɗaɗi. |
|