نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3275 | 28 | 23 | ولما ورد ماء مدين وجد عليه أمة من الناس يسقون ووجد من دونهم امرأتين تذودان قال ما خطبكما قالتا لا نسقي حتى يصدر الرعاء وأبونا شيخ كبير |
| | | Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho ne mai daraja." |
|
3276 | 28 | 24 | فسقى لهما ثم تولى إلى الظل فقال رب إني لما أنزلت إلي من خير فقير |
| | | Sai ya shãyar musu, sa'an nan kuma ya jũya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alhẽri ni mai bukãta ne." |
|
3277 | 28 | 25 | فجاءته إحداهما تمشي على استحياء قالت إن أبي يدعوك ليجزيك أجر ما سقيت لنا فلما جاءه وقص عليه القصص قال لا تخف نجوت من القوم الظالمين |
| | | Sai ɗayansu ta je masa, tanã tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubãna yanã kiran ka, dõmin ya sãka maka ijãrar abin da ka shãyar sabõda mu." To, a lõkacin da ya je masa, ya gaya masa lãbãrinsa, ya ce: "Kada ka ji tsõro, kã tsĩra daga mutãne azzãlumai." |
|
3278 | 28 | 26 | قالت إحداهما يا أبت استأجره إن خير من استأجرت القوي الأمين |
| | | ¦ayarsu ta ce, "Yã Bãba! Ka bã shi aikin ijãra, lalle ne mafi alhẽrin wanda ka bai wa aikin ijãra shi ne mai ƙarfi amintacce." |
|
3279 | 28 | 27 | قال إني أريد أن أنكحك إحدى ابنتي هاتين على أن تأجرني ثماني حجج فإن أتممت عشرا فمن عندك وما أريد أن أشق عليك ستجدني إن شاء الله من الصالحين |
| | | Ya ce: "Lalle ne inã nufin in aurar da kai ɗayan 'yã'yãna biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijãra shẽkara takwas to, idan ka cika gõma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsanantã maka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga sãlihai." |
|
3280 | 28 | 28 | قال ذلك بيني وبينك أيما الأجلين قضيت فلا عدوان علي والله على ما نقول وكيل |
| | | Ya ce: "Wannan yanã a tsakanina da tsakãninka kõwane ɗayan adadin biyun na ƙãre, to, bãbu wani zãlunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa." |
|
3281 | 28 | 29 | فلما قضى موسى الأجل وسار بأهله آنس من جانب الطور نارا قال لأهله امكثوا إني آنست نارا لعلي آتيكم منها بخبر أو جذوة من النار لعلكم تصطلون |
| | | To, a lokacin da Mũsã ya ƙãre adadin kuma yanã tafiya da iyãlinsa, sai ya tsinkãyi wata Wutã daga gẽfen dũtse (¦ũr). Ya cewa iyãlinsa, "Ku dãkata, lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wutã, tsammãnĩna ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani lãbãrĩ, kõ kuwa da guntun makãmashi daga Wutar don kõ ku ji ɗimi." |
|
3282 | 28 | 30 | فلما أتاها نودي من شاطئ الواد الأيمن في البقعة المباركة من الشجرة أن يا موسى إني أنا الله رب العالمين |
| | | To, a lõkacin da ya jẽ wurinta (Wutar) aka kirã shi, daga gẽfen rãfin na dãma, a cikin wurin nan mai albarka, daga itãciyar (cẽwa) "Ya Mũsã! Lalle Nĩ ne Allah Ubangijin halittu." |
|
3283 | 28 | 31 | وأن ألق عصاك فلما رآها تهتز كأنها جان ولى مدبرا ولم يعقب يا موسى أقبل ولا تخف إنك من الآمنين |
| | | "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta, tanã girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya jũya yanã mai bãyar da bãya, bai kõma ba. "Ya Mũsã! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsõro lalle ne kanã daga waɗanda ke amintattu." |
|
3284 | 28 | 32 | اسلك يدك في جيبك تخرج بيضاء من غير سوء واضمم إليك جناحك من الرهب فذانك برهانان من ربك إلى فرعون وملئه إنهم كانوا قوما فاسقين |
| | | "Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rĩgarka, ya fita fari, ba da wata cũta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kãfaɗunka, dõmin tsõro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abũbuwa dalĩlai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutãne ne fãsiƙai." |
|