نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3249 | 27 | 90 | ومن جاء بالسيئة فكبت وجوههم في النار هل تجزون إلا ما كنتم تعملون |
| | | Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa? |
|
3250 | 27 | 91 | إنما أمرت أن أعبد رب هذه البلدة الذي حرمها وله كل شيء وأمرت أن أكون من المسلمين |
| | | (Ka ce): "An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa." |
|
3251 | 27 | 92 | وأن أتلو القرآن فمن اهتدى فإنما يهتدي لنفسه ومن ضل فقل إنما أنا من المنذرين |
| | | "Kuma inã karanta Alƙur'ãni." To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: "Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake." |
|
3252 | 27 | 93 | وقل الحمد لله سيريكم آياته فتعرفونها وما ربك بغافل عما تعملون |
| | | Kuma ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu." Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba. |
|
3253 | 28 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طسم |
| | | ¦. S̃. M̃. |
|
3254 | 28 | 2 | تلك آيات الكتاب المبين |
| | | Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne. |
|
3255 | 28 | 3 | نتلو عليك من نبإ موسى وفرعون بالحق لقوم يؤمنون |
| | | Munã karantãwa a kanka daga lãbarin Mũsã da Fir'auna da gaskiya dõmin mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. |
|
3256 | 28 | 4 | إن فرعون علا في الأرض وجعل أهلها شيعا يستضعف طائفة منهم يذبح أبناءهم ويستحيي نساءهم إنه كان من المفسدين |
| | | Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutãnenta ƙungiya-ƙungiya, yanã raunanar da wata jama'a daga gare su; yanã yanyanka ɗiyansu maza kuma yanã rãyar da mãtan. Lalle shĩ ya kasance daga mãsu ɓarna. |
|
3257 | 28 | 5 | ونريد أن نمن على الذين استضعفوا في الأرض ونجعلهم أئمة ونجعلهم الوارثين |
| | | Kuma Munã nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magãda. |
|
3258 | 28 | 6 | ونمكن لهم في الأرض ونري فرعون وهامان وجنودهما منهم ما كانوا يحذرون |
| | | Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nũna wa Fir'auna da Hãmãna da rundunõninsu abin da suka kasance sunã sauna daga gare su. |
|