نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3233 | 27 | 74 | وإن ربك ليعلم ما تكن صدورهم وما يعلنون |
| | | Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa. |
|
3234 | 27 | 75 | وما من غائبة في السماء والأرض إلا في كتاب مبين |
| | | Kuma bãbu wata (mas'ala) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne. |
|
3235 | 27 | 76 | إن هذا القرآن يقص على بني إسرائيل أكثر الذي هم فيه يختلفون |
| | | Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki. |
|
3236 | 27 | 77 | وإنه لهدى ورحمة للمؤمنين |
| | | Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai. |
|
3237 | 27 | 78 | إن ربك يقضي بينهم بحكمه وهو العزيز العليم |
| | | "Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani." |
|
3238 | 27 | 79 | فتوكل على الله إنك على الحق المبين |
| | | Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya. |
|
3239 | 27 | 80 | إنك لا تسمع الموتى ولا تسمع الصم الدعاء إذا ولوا مدبرين |
| | | Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya. |
|
3240 | 27 | 81 | وما أنت بهادي العمي عن ضلالتهم إن تسمع إلا من يؤمن بآياتنا فهم مسلمون |
| | | Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa (al'amari zuwa ga Allah). |
|
3241 | 27 | 82 | وإذا وقع القول عليهم أخرجنا لهم دابة من الأرض تكلمهم أن الناس كانوا بآياتنا لا يوقنون |
| | | Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa "Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni." |
|
3242 | 27 | 83 | ويوم نحشر من كل أمة فوجا ممن يكذب بآياتنا فهم يوزعون |
| | | Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. (ga kõra) |
|