نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3183 | 27 | 24 | وجدتها وقومها يسجدون للشمس من دون الله وزين لهم الشيطان أعمالهم فصدهم عن السبيل فهم لا يهتدون |
| | | "Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa." |
|
3184 | 27 | 25 | ألا يسجدوا لله الذي يخرج الخبء في السماوات والأرض ويعلم ما تخفون وما تعلنون |
| | | "Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwada abin da kuke bayyanãwa." |
|
3185 | 27 | 26 | الله لا إله إلا هو رب العرش العظيم |
| | | "Allah bãbu abin bautãwa fãce shĩ Ubangijin Al'arshi, mai girma." |
|
3186 | 27 | 27 | قال سننظر أصدقت أم كنت من الكاذبين |
| | | Ya ce: "Za mu dũba shin kã yi gaskiya ne, kõ kuwa kã kasance daga maƙaryata?" |
|
3187 | 27 | 28 | اذهب بكتابي هذا فألقه إليهم ثم تول عنهم فانظر ماذا يرجعون |
| | | "Ka tafi da takardata wannan, sa'an nan ka jẽfa ta zuwa gare su, sa'an nan kuma ka jũya daga barinsu, sa'an nan ka ga mẽne ne suke mayarwa." |
|
3188 | 27 | 29 | قالت يا أيها الملأ إني ألقي إلي كتاب كريم |
| | | Ta ce: "Yã kũ mashawarta! Lalle ne, an jẽfo, zuwa gareni, wata takarda mai girma." |
|
3189 | 27 | 30 | إنه من سليمان وإنه بسم الله الرحمن الرحيم |
| | | "Lalle ita daga Sulaiman take, kuma lalle ita da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai ne." |
|
3190 | 27 | 31 | ألا تعلوا علي وأتوني مسلمين |
| | | "Kada ku yi girman kai a gare ni, kuma ku zo mini kunã mãsu sallamãwa." |
|
3191 | 27 | 32 | قالت يا أيها الملأ أفتوني في أمري ما كنت قاطعة أمرا حتى تشهدون |
| | | Ta ce: "Yã ku mashawarta! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta." |
|
3192 | 27 | 33 | قالوا نحن أولو قوة وأولو بأس شديد والأمر إليك فانظري ماذا تأمرين |
| | | Suka ce: "Mũ ma'abũta ƙarfi ne, kuma ma'abbũta yãƙi mai tsanani ne, kuma al'amari yã kõma zuwa gare ki, sabõda haka ki dũbamẽne ne zã ki yi umurui (da shi)?" |
|