نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3160 | 27 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طس تلك آيات القرآن وكتاب مبين |
| | | ¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa. |
|
3161 | 27 | 2 | هدى وبشرى للمؤمنين |
| | | Shiriya ce da bushãra ga mũminai. |
|
3162 | 27 | 3 | الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم بالآخرة هم يوقنون |
| | | Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni. |
|
3163 | 27 | 4 | إن الذين لا يؤمنون بالآخرة زينا لهم أعمالهم فهم يعمهون |
| | | Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa. |
|
3164 | 27 | 5 | أولئك الذين لهم سوء العذاب وهم في الآخرة هم الأخسرون |
| | | Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra. |
|
3165 | 27 | 6 | وإنك لتلقى القرآن من لدن حكيم عليم |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa, anã haɗa ka da Alƙur'ãni daga gun Mai hikima, Masani. |
|
3166 | 27 | 7 | إذ قال موسى لأهله إني آنست نارا سآتيكم منها بخبر أو آتيكم بشهاب قبس لعلكم تصطلون |
| | | A lõkacin da Mũsã ya ce wa iyãlinsa "Lalle ni, na tsinkãyi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani lãbari, ko kuwa mai zo muku ne da Yũla, makãmashi, tsammãninku, ku ji ɗimi." |
|
3167 | 27 | 8 | فلما جاءها نودي أن بورك من في النار ومن حولها وسبحان الله رب العالمين |
| | | To, a lõkacin da ya jẽ mata, sai aka kira shi cẽwa, "An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da yanda yake a gẽfenta kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu." |
|
3168 | 27 | 9 | يا موسى إنه أنا الله العزيز الحكيم |
| | | "Yã Mũsã lalle ne shi, Nĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima." |
|
3169 | 27 | 10 | وألق عصاك فلما رآها تهتز كأنها جان ولى مدبرا ولم يعقب يا موسى لا تخف إني لا يخاف لدي المرسلون |
| | | "Kuma ka jẽfa sandarka." To, a lõkacin da ya gan ta tanã girgiza kamar dai ita ƙaramin macĩji ne, sai ya jũya yanã mai bãyar da bãya, kuma bai kõma ba, "Yã Musã! Kada ka ji tsõro lalle Ni, Manzanni bã sujin tsõro a wuriNa." |
|