نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3155 | 26 | 223 | يلقون السمع وأكثرهم كاذبون |
| | | Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne. |
|
3156 | 26 | 224 | والشعراء يتبعهم الغاوون |
| | | Kuma mawãƙa halakakku ne ke bin su. |
|
3157 | 26 | 225 | ألم تر أنهم في كل واد يهيمون |
| | | Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba? |
|
3158 | 26 | 226 | وأنهم يقولون ما لا يفعلون |
| | | Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa? |
|
3159 | 26 | 227 | إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وذكروا الله كثيرا وانتصروا من بعد ما ظلموا وسيعلم الذين ظلموا أي منقلب ينقلبون |
| | | Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa. |
|
3160 | 27 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم طس تلك آيات القرآن وكتاب مبين |
| | | ¦. S̃. Waɗancan ãyõyinAlƙur'ãni ne da Littãfi mai bayyanawa. |
|
3161 | 27 | 2 | هدى وبشرى للمؤمنين |
| | | Shiriya ce da bushãra ga mũminai. |
|
3162 | 27 | 3 | الذين يقيمون الصلاة ويؤتون الزكاة وهم بالآخرة هم يوقنون |
| | | Waɗanda suke tsayar da salla kuma su bãyar da zakka, alhãli kuwa sũ, game da Lãhira, to, sũ, sunã yin yaƙĩni. |
|
3163 | 27 | 4 | إن الذين لا يؤمنون بالآخرة زينا لهم أعمالهم فهم يعمهون |
| | | Lalle ne waɗanda suke bã su yin ĩmãni da Lãhira, Mun ƙawãta musu ayyukansu, sabõda haka sunã ɗimuwa. |
|
3164 | 27 | 5 | أولئك الذين لهم سوء العذاب وهم في الآخرة هم الأخسرون |
| | | Waɗannan ne waɗanda suke sunã da mugunyar azãba (a dũniya), kuma sũ, a Lãhira, sũ ne mafiya hasãra. |
|