نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3125 | 26 | 193 | نزل به الروح الأمين |
| | | Rũhi amintacce ne ya sauka da shi. |
|
3126 | 26 | 194 | على قلبك لتكون من المنذرين |
| | | A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi. |
|
3127 | 26 | 195 | بلسان عربي مبين |
| | | Da harshe na Larabci mai bayãni. |
|
3128 | 26 | 196 | وإنه لفي زبر الأولين |
| | | Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko. |
|
3129 | 26 | 197 | أولم يكن لهم آية أن يعلمه علماء بني إسرائيل |
| | | Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi? |
|
3130 | 26 | 198 | ولو نزلناه على بعض الأعجمين |
| | | Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa, |
|
3131 | 26 | 199 | فقرأه عليهم ما كانوا به مؤمنين |
| | | Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba. |
|
3132 | 26 | 200 | كذلك سلكناه في قلوب المجرمين |
| | | Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. |
|
3133 | 26 | 201 | لا يؤمنون به حتى يروا العذاب الأليم |
| | | Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi. |
|
3134 | 26 | 202 | فيأتيهم بغتة وهم لا يشعرون |
| | | Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba. |
|