نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3103 | 26 | 171 | إلا عجوزا في الغابرين |
| | | Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa. |
|
3104 | 26 | 172 | ثم دمرنا الآخرين |
| | | Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu. |
|
3105 | 26 | 173 | وأمطرنا عليهم مطرا فساء مطر المنذرين |
| | | Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. |
|
3106 | 26 | 174 | إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba. |
|
3107 | 26 | 175 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|
3108 | 26 | 176 | كذب أصحاب الأيكة المرسلين |
| | | Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni. |
|
3109 | 26 | 177 | إذ قال لهم شعيب ألا تتقون |
| | | A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" |
|
3110 | 26 | 178 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce." |
|
3111 | 26 | 179 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3112 | 26 | 180 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." |
|