نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3096 | 26 | 164 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." |
|
3097 | 26 | 165 | أتأتون الذكران من العالمين |
| | | "Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai?" |
|
3098 | 26 | 166 | وتذرون ما خلق لكم ربكم من أزواجكم بل أنتم قوم عادون |
| | | "Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa!" |
|
3099 | 26 | 167 | قالوا لئن لم تنته يا لوط لتكونن من المخرجين |
| | | Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)." |
|
3100 | 26 | 168 | قال إني لعملكم من القالين |
| | | Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa." |
|
3101 | 26 | 169 | رب نجني وأهلي مما يعملون |
| | | "Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa." |
|
3102 | 26 | 170 | فنجيناه وأهله أجمعين |
| | | Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya. |
|
3103 | 26 | 171 | إلا عجوزا في الغابرين |
| | | Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa. |
|
3104 | 26 | 172 | ثم دمرنا الآخرين |
| | | Sa'an nan kuma Muka darkãke wasu. |
|
3105 | 26 | 173 | وأمطرنا عليهم مطرا فساء مطر المنذرين |
| | | Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana. |
|