نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3080 | 26 | 148 | وزروع ونخل طلعها هضيم |
| | | "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?" |
|
3081 | 26 | 149 | وتنحتون من الجبال بيوتا فارهين |
| | | "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?" |
|
3082 | 26 | 150 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3083 | 26 | 151 | ولا تطيعوا أمر المسرفين |
| | | "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata." |
|
3084 | 26 | 152 | الذين يفسدون في الأرض ولا يصلحون |
| | | "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa." |
|
3085 | 26 | 153 | قالوا إنما أنت من المسحرين |
| | | Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake." |
|
3086 | 26 | 154 | ما أنت إلا بشر مثلنا فأت بآية إن كنت من الصادقين |
| | | "Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
|
3087 | 26 | 155 | قال هذه ناقة لها شرب ولكم شرب يوم معلوم |
| | | Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan yini, kuma kunã da shan yini sasanne." |
|
3088 | 26 | 156 | ولا تمسوها بسوء فيأخذكم عذاب يوم عظيم |
| | | "Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku." |
|
3089 | 26 | 157 | فعقروها فأصبحوا نادمين |
| | | Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma. |
|