نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3075 | 26 | 143 | إني لكم رسول أمين |
| | | "Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce." |
|
3076 | 26 | 144 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã. |
|
3077 | 26 | 145 | وما أسألكم عليه من أجر إن أجري إلا على رب العالمين |
| | | "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu." |
|
3078 | 26 | 146 | أتتركون في ما هاهنا آمنين |
| | | "Shin, anã barin ku a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu?" |
|
3079 | 26 | 147 | في جنات وعيون |
| | | "A cikin gõnaki da marẽmari." |
|
3080 | 26 | 148 | وزروع ونخل طلعها هضيم |
| | | "Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi mãsu narkẽwa a ciki?" |
|
3081 | 26 | 149 | وتنحتون من الجبال بيوتا فارهين |
| | | "Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari?" |
|
3082 | 26 | 150 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3083 | 26 | 151 | ولا تطيعوا أمر المسرفين |
| | | "Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata." |
|
3084 | 26 | 152 | الذين يفسدون في الأرض ولا يصلحون |
| | | "Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa." |
|