نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3063 | 26 | 131 | فاتقوا الله وأطيعون |
| | | "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." |
|
3064 | 26 | 132 | واتقوا الذي أمدكم بما تعلمون |
| | | "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani." |
|
3065 | 26 | 133 | أمدكم بأنعام وبنين |
| | | "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya." |
|
3066 | 26 | 134 | وجنات وعيون |
| | | "Da gõnaki da marẽmari." |
|
3067 | 26 | 135 | إني أخاف عليكم عذاب يوم عظيم |
| | | "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma." |
|
3068 | 26 | 136 | قالوا سواء علينا أوعظت أم لم تكن من الواعظين |
| | | Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba." |
|
3069 | 26 | 137 | إن هذا إلا خلق الأولين |
| | | "Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen mutãnen farko." |
|
3070 | 26 | 138 | وما نحن بمعذبين |
| | | "Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba." |
|
3071 | 26 | 139 | فكذبوه فأهلكناهم إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba. |
|
3072 | 26 | 140 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|