نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3045 | 26 | 113 | إن حسابهم إلا على ربي لو تشعرون |
| | | "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." |
|
3046 | 26 | 114 | وما أنا بطارد المؤمنين |
| | | "Ban zama mai kõre mũminai ba." |
|
3047 | 26 | 115 | إن أنا إلا نذير مبين |
| | | "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." |
|
3048 | 26 | 116 | قالوا لئن لم تنته يا نوح لتكونن من المرجومين |
| | | Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa" |
|
3049 | 26 | 117 | قال رب إن قومي كذبون |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni." |
|
3050 | 26 | 118 | فافتح بيني وبينهم فتحا ونجني ومن معي من المؤمنين |
| | | "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai." |
|
3051 | 26 | 119 | فأنجيناه ومن معه في الفلك المشحون |
| | | Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi. |
|
3052 | 26 | 120 | ثم أغرقنا بعد الباقين |
| | | Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran. |
|
3053 | 26 | 121 | إن في ذلك لآية وما كان أكثرهم مؤمنين |
| | | Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. |
|
3054 | 26 | 122 | وإن ربك لهو العزيز الرحيم |
| | | Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama. |
|