نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3043 | 26 | 111 | قالوا أنؤمن لك واتبعك الأرذلون |
| | | Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?" |
|
3044 | 26 | 112 | قال وما علمي بما كانوا يعملون |
| | | Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa." |
|
3045 | 26 | 113 | إن حسابهم إلا على ربي لو تشعرون |
| | | "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." |
|
3046 | 26 | 114 | وما أنا بطارد المؤمنين |
| | | "Ban zama mai kõre mũminai ba." |
|
3047 | 26 | 115 | إن أنا إلا نذير مبين |
| | | "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." |
|
3048 | 26 | 116 | قالوا لئن لم تنته يا نوح لتكونن من المرجومين |
| | | Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa" |
|
3049 | 26 | 117 | قال رب إن قومي كذبون |
| | | Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni." |
|
3050 | 26 | 118 | فافتح بيني وبينهم فتحا ونجني ومن معي من المؤمنين |
| | | "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai." |
|
3051 | 26 | 119 | فأنجيناه ومن معه في الفلك المشحون |
| | | Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi. |
|
3052 | 26 | 120 | ثم أغرقنا بعد الباقين |
| | | Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran. |
|