نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3019 | 26 | 87 | ولا تخزني يوم يبعثون |
| | | "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su." |
|
3020 | 26 | 88 | يوم لا ينفع مال ولا بنون |
| | | "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi." |
|
3021 | 26 | 89 | إلا من أتى الله بقلب سليم |
| | | "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki." |
|
3022 | 26 | 90 | وأزلفت الجنة للمتقين |
| | | Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa. |
|
3023 | 26 | 91 | وبرزت الجحيم للغاوين |
| | | Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku. |
|
3024 | 26 | 92 | وقيل لهم أين ما كنتم تعبدون |
| | | Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?" |
|
3025 | 26 | 93 | من دون الله هل ينصرونكم أو ينتصرون |
| | | "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?" |
|
3026 | 26 | 94 | فكبكبوا فيها هم والغاوون |
| | | Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun. |
|
3027 | 26 | 95 | وجنود إبليس أجمعون |
| | | Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya. |
|
3028 | 26 | 96 | قالوا وهم فيها يختصمون |
| | | Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, |
|