نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
3006 | 26 | 74 | قالوا بل وجدنا آباءنا كذلك يفعلون |
| | | Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa." |
|
3007 | 26 | 75 | قال أفرأيتم ما كنتم تعبدون |
| | | Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?" |
|
3008 | 26 | 76 | أنتم وآباؤكم الأقدمون |
| | | "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?" |
|
3009 | 26 | 77 | فإنهم عدو لي إلا رب العالمين |
| | | "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu." |
|
3010 | 26 | 78 | الذي خلقني فهو يهدين |
| | | "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni." |
|
3011 | 26 | 79 | والذي هو يطعمني ويسقين |
| | | "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni." |
|
3012 | 26 | 80 | وإذا مرضت فهو يشفين |
| | | "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni." |
|
3013 | 26 | 81 | والذي يميتني ثم يحيين |
| | | "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni." |
|
3014 | 26 | 82 | والذي أطمع أن يغفر لي خطيئتي يوم الدين |
| | | "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako." |
|
3015 | 26 | 83 | رب هب لي حكما وألحقني بالصالحين |
| | | "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai." |
|