نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2976 | 26 | 44 | فألقوا حبالهم وعصيهم وقالوا بعزة فرعون إنا لنحن الغالبون |
| | | Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." |
|
2977 | 26 | 45 | فألقى موسى عصاه فإذا هي تلقف ما يأفكون |
| | | Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya. |
|
2978 | 26 | 46 | فألقي السحرة ساجدين |
| | | Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada. |
|
2979 | 26 | 47 | قالوا آمنا برب العالمين |
| | | Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta." |
|
2980 | 26 | 48 | رب موسى وهارون |
| | | "Ubangijin Mũsa da Hãrũna." |
|
2981 | 26 | 49 | قال آمنتم له قبل أن آذن لكم إنه لكبيركم الذي علمكم السحر فلسوف تعلمون لأقطعن أيديكم وأرجلكم من خلاف ولأصلبنكم أجمعين |
| | | Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya." |
|
2982 | 26 | 50 | قالوا لا ضير إنا إلى ربنا منقلبون |
| | | Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu." |
|
2983 | 26 | 51 | إنا نطمع أن يغفر لنا ربنا خطايانا أن كنا أول المؤمنين |
| | | "Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni." |
|
2984 | 26 | 52 | وأوحينا إلى موسى أن أسر بعبادي إنكم متبعون |
| | | Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne. |
|
2985 | 26 | 53 | فأرسل فرعون في المدائن حاشرين |
| | | Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne. |
|