نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2970 | 26 | 38 | فجمع السحرة لميقات يوم معلوم |
| | | Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne. |
|
2971 | 26 | 39 | وقيل للناس هل أنتم مجتمعون |
| | | Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne? |
|
2972 | 26 | 40 | لعلنا نتبع السحرة إن كانوا هم الغالبين |
| | | "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya." |
|
2973 | 26 | 41 | فلما جاء السحرة قالوا لفرعون أئن لنا لأجرا إن كنا نحن الغالبين |
| | | To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?" |
|
2974 | 26 | 42 | قال نعم وإنكم إذا لمن المقربين |
| | | Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai." |
|
2975 | 26 | 43 | قال لهم موسى ألقوا ما أنتم ملقون |
| | | Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa." |
|
2976 | 26 | 44 | فألقوا حبالهم وعصيهم وقالوا بعزة فرعون إنا لنحن الغالبون |
| | | Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." |
|
2977 | 26 | 45 | فألقى موسى عصاه فإذا هي تلقف ما يأفكون |
| | | Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya. |
|
2978 | 26 | 46 | فألقي السحرة ساجدين |
| | | Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada. |
|
2979 | 26 | 47 | قالوا آمنا برب العالمين |
| | | Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta." |
|