نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
2967 | 26 | 35 | يريد أن يخرجكم من أرضكم بسحره فماذا تأمرون |
| | | "Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa?" |
|
2968 | 26 | 36 | قالوا أرجه وأخاه وابعث في المدائن حاشرين |
| | | Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne." |
|
2969 | 26 | 37 | يأتوك بكل سحار عليم |
| | | "Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani." |
|
2970 | 26 | 38 | فجمع السحرة لميقات يوم معلوم |
| | | Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne. |
|
2971 | 26 | 39 | وقيل للناس هل أنتم مجتمعون |
| | | Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne? |
|
2972 | 26 | 40 | لعلنا نتبع السحرة إن كانوا هم الغالبين |
| | | "Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya." |
|
2973 | 26 | 41 | فلما جاء السحرة قالوا لفرعون أئن لنا لأجرا إن كنا نحن الغالبين |
| | | To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya?" |
|
2974 | 26 | 42 | قال نعم وإنكم إذا لمن المقربين |
| | | Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai." |
|
2975 | 26 | 43 | قال لهم موسى ألقوا ما أنتم ملقون |
| | | Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa." |
|
2976 | 26 | 44 | فألقوا حبالهم وعصيهم وقالوا بعزة فرعون إنا لنحن الغالبون |
| | | Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya." |
|